<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu, ga ni gabanka,
 Domin in koyi gaskiyarka.
 Ka nuna mini cin gaba
 Da ni zan yi a hanyarka.

[V2]
 KORUS
 Ya Yesu, buɗe idona,
 Domin in gane hanyarka,
 Ka nuna mini nufinka,
 Ya Mai Ceto.

[V3]
 2) Ya Yesu, buɗe kunnena,
 Domin in ji maganarka.
 Ni ina so in bi nufinka,
 In yi abin da ka ke so.

[V4]
 KORUS
 Ya Yesu, buɗe kunnena,
 Domin in ji maganarka,
 Ka nuna mini nufinka,
 Ya Mai Ceto.

[V5]
 3) Ya Yesu, buɗe bakina,
 Domin in shaida ko'ina
 Ceton da ka yi wa duniya
 Da gafarar zunubanmu.

[V6]
 KORUS
 Ya Yesu, buɗe bakina,
 Domin in shaida cetonka,
 Ka nuna mini nufinka,
 Ya Mai Ceto.

[V7]
 4) Yesu, juyad da zuciyata,
 Domin in nuna halinka
 Ƴanuwana su dube ni,
 Har su ga Allah cikina.

[V8]
 KORUS
 Yesu, juyad da zuciyata
 Domin in nuna halinka,
 Ka nuna mini nufinka,
 Ya Mai Ceto.

[V9]
 5) Ya Yesu, ba ni zarafi
 Domin in yi ta aikinka,
 Ƴanuwana su rinjayu
 Su ma su shiga hanyarka.

[V10]
 KORUS
 Ya Yesu, ba ni zarafi
 Domin in yi ta aikinka,
 Ka nuna mini nufinka,
 Ya Mai Ceto.</lyrics>
<title>Ya Yesu, Ga Ni Gabanka LW211</title>
<hymn_number>211</hymn_number>
</song>